Benitez zai ci gaba da horar da Newcastle

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Newcastle United za ta buga gasar Championship a badi

Rafael Benitez zai ci gaba da zama a matsayin kociyan Newcastle United, bayan da ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku.

Benitez mai shekara 55, ya karbi aikin horar da Newcastle a cikin watan Maris, bayan da ya maye gurbin Steve McClaren wanda aka kora daga aikin.

A yarjejeniyar da ya kulla da Newcastle a baya, an fayyace cewar kociyan zai iya barin kungiyar idan ta fadi daga gasar Premier bana.

Benitez wanda ya horar da Valencia da Liverpool da Inter Milan da Chelsea da Napoli da kuma Real Madrid ya karbi aikin horar da Newcastle a lokacin da take daf da faduwa daga gasar Premier.

Kociyan ya ci wasanni uku daga guda 10 da ya jagoranci kungiyar wadda ta fadi daga gasar Premier shekarar nan.