Sturridge bai halarci atisaye ba

Hakkin mallakar hoto AFPGetty
Image caption Faransa ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai

Dan kwallon Liverpool Daniel Sturridge bai je atisaye a tawagar kwallon kafa ta Ingila a ranar Laraba ba.

Dan wasan, mai shekara 26, bai buga wasan sada zumuntar da Ingila ta ci Turkiya 2-1 ba, sakamakon jinyar da yake yi.

Watakila dan wasan Manchester United, Marcus Rashford ya buga wasan da Ingila za ta yi na sada zumunta da Australia ranar Jumaa.

Kociyan tawagar Ingila Roy Hodgson zai bayyana sunayen yan wasa 23 da za su wakilci kasar a gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan kammala karawa da Australia.

A makon jiya ne kociyan ya sanar da sunayen yan wasa 26 na tawagar ta Ingila na kwar-ya-kwar-ya.