An daidaita tsakanin Mourinho da United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ce ta dauki kofin Kalubale na bana kuma na 12 jumulla

An cimma matsaya cewar Jose Mourinho zai zama kociyan Manchester United, bayan kwanaki uku ana tattaunawa.

Tuni dai wakilin Mourinho, Jorge Mendes da manyan jami'an United suka cimma matsaya, amma ba a kai ga saka hannu kan yarjejeniya ba.

A ranar Juma'a ne ake sa ran Manchester United za ta sanar da nada Mourinho a matsayin sabon kociyanta.

Mourinho zai maye gurbin Louis van Gaal wanda aka kora daga aikin horar da United a ranar Litinin.

Tun a ranar Talata aka fara tattaunawa tsakanin United da Mourinho, amma takaddama kan hakkin mallakar tallar Mourinho ta kawo tsaiko.