Real Madrid za ta kara da Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Real Madrid ta dauki kofin zakarun Turai guda 10

Real Madrid za ta fafata da Atletico Madrid a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai a ranar Asabar a filin wasa na San Siro da ke Italiya.

Real Madrid ta kai wasan karshe ne a gasar bana, bayan da ta doke Manchester City da ci daya mai ban haushi a karawa biyu da suka yi.

Ita kuwa Atletico ta kai matsayin ne bayan da ta samu nasara a kan Bayern Munich, inda a gidanta ta ci 1-0 a Jamus aka doke ta 2-1.

Karawar da za a yi tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid a wasan karshe a gasar zakarun Turai, maimaicin wadda suka yi a 2014 ce, in da Real ta ci wasan 4-1.

Kungiyoyin biyu da ke buga gasar La Ligar Spaniya sun kara a gasar bana, inda suka tashi 1-1 a ranar 4 ga watan Oktoba a gidan Atletico.

Amma kuma a wasa na biyu Atletico ce ta ci Madrid 1-0 a karawar da suka yi ranar 27 ga watan Fabrairun 2016.

Real Madrid ta dauki kofin zakarun Turai sau 10, yayin da Atletico Madrid ba ta taba daukar kofin ba.