Ibrahimovic ya zabi inda zai yi wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ake sa ran zai maye gurbin Louis van Gaal a United

Dan kwallon tawagar Sweden, Zlatan Ibrahimovic, ya ce tuni ya san inda zai koma da ci gaba da buga tamaula.

Amma ya yi shiru ne domin yaga yadda za ta kaya a batun da ake yi cewar Manchester United na zawarcinsa.

Jose Mourinho wanda ya horar da Ibrahimovic shekara daya a Inter Milan, na daf da zama kociyan Manchester United.

Ibrahimovic mai shekara 34, wadda ya bar Paris St-Germain a karshen kakar wasan bana, ya ce ya samu ta yi daga manyan kungiyoyin kwallon kafa da ke fadin duniyar nan.

Ibrahimovic tsohon dan wasan Paris Saint-Germain da Malmö da Ajax da Juventus da Inter Milan da Barcelona da kuma Milan.