Ko Rashford zai je Euro 2016?

Hakkin mallakar hoto REX FEATUES
Image caption Rashford yana murnar cin kwallo

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Ingila, sun yi wa Marcus Rashford tafin ban girma, a tsakiyar filin wasa na Light da ke Sunderland bayan ya yi bajintar da ta burge, a fafatawar da suka cinye Australia.

Dan wasan gaba na Manchester United, mai shekara 18, ya kafa tarihi a matsayin zakaran cin kwallo a wasansa na farko da ya buga wa Ingila.

Rashford dai ya jefa kwallo ta biyu a kasa da minti 3, a wasan da suka yi nasara da ci 2-1 a kan Australia.

Hakan ne ya sa ake son a sa sunansa a jerin 'yan wasa 23 da kocin Ingila Roy Hodgson zai fitar don gasar cin kofin kasashen Turai ta 2016.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ko a wasansa na farko da ya buga wa Man U ma, Rashford ya ci kwallaye biyu

Ko wannan matashi da tauraruwarsa take haskawa a Old Trafford zai samu damar sanya kafarsa a gasar kasashen duniya da za a yi a Faransa?

Lokacin da Roy Hodgson ya ambaci sunan Rashford a ayarin 'yan wasansa na farko mai mutum 26, ranar 16 ga watan Mayu, an dauka cewa matashin na daya daga cikin wadanda za a rage.

Ana ganinsa a matsayin daya daga cikin manyan gobe, wanda zai bi sahun John Stones na Everton da Jon Flanagan na Liverpool kafin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2014 a Brazil.

Halin da ake ciki ya sauya al'amura, don kuwa a yanzu akwai matukar yiwuwa cewa Hodgson ba zai iya bijire wa kiraye-kirayen da magoya baya ke yi ba na a sanya matashin cikin ayarin Ingila da zai fitar ranar Talata.