Real da Atletico za su yi karon battar karfe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Torres ya ce tun yana dan shekara biyar yake goyon bayan Atletico kafin ya fara buga mata wasa

Dan wasan gaba na Atletico Madrid, Fernando Torres ya yi imani cewa karon battar karshe ta gasar zakarun Turai da Real Madrid shi ne wasa mafi muhimmanci a rayuwarsa.

Dan kasar Spaniyan mai shekara 32 ya lashe gasar zakarun Turai a Chelsea cikin 2012, ya ci kuma kofin duniya da ta Turai, ko da yake, a duk zamansa a Atletico bai taba cin babbar gasa ba.

Sai dai, gogan naka ya ce wasan ranar Asabar daban ne, kuma muhimmi ne. Don kuwa Atletico ne ya ba shi damar fara sana'arsa ta murza leda.

A shekara ta 2014, Real Madrid ta dauki kofin zakarun Turai a hannun Atletico bayan ta yi nasara a kan ta da ci 4-1.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ronaldo ya ce yana da koshin lafiyar da zai kai Real ga nasara

Akwai dai fargaba kan matsayin lafiyar Ronaldo, wanda ya ci kwallo 16 a gasar, adadin da ya kai yawan kwallayen duk 'yan Atletico, yana kuma iya dorawa kan tarihinsa na cin kwallo 17 a kaka.

Sai dai duk da kammala La Liga da maki biyu a saman Atletico, sau daya Real Madrid ta cinye kulob din Simeone a karawa shida na baya-bayan nan.

Simeone ya kai Atletico Madrid cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai tun bayan nada shi a matsayin kocin kungiyar a 2011.

Rawar ganin da kungiyar ta yi wajen doke Barcelona da Bayern Munich a kan hanyar zuwa wasan karshe ya janyo mata yabo da jinjina.

An ci kungiyar kwallo 7 a kan hanyarta ta zuwa wasan karshe, sai kuma kwallo 2 da aka jefa mata a wasanni 9 na karshe da ta buga a kakar bana.

Yayin da Atletico ke cike ratar da Real ta ba ta a gida, wasan yau a filin San Siro zai ba ta damar lashe kofin zakarun Turai karon farko a cikin shekara 113, yayin da Real ke kokarin cin kofin karo na 11.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Idan Zidane ya ci wasan na yau, Real za ta kasance a gaban Milan da yawan kofin karo 4

Kungiyar ta Zidane ta yi rashin nasara sau biyu a wasa 26 da ta buga tun lokacin da ya gaji Rafael Benitez, Atletico kuma na cikin kungiyoyi biyu da suka lallasa Real.

Zidane dai ya ce ba gazawa ba ce idan aka cinye su, kawai abin da zai iya cewa shi ne sun shirya.

Real da Atletico sun yi wasa sau 40, Real ta yi nasara sau 23, ita kuma Atletico sau 7, Real ta yi rashin nasara sau 7, ita kuma sau 23, haka kuma sun yi canjaras sau 10.