U-23: Tawagar Nigeria ta isa Korea

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar 5 ga Agusta ne za a fara gasar Olympics a Rio

Tawagar kwallon kafa ta matasa ‘yan kasa da shekara 23 ta Nigeria ta isa Korea domin fara wasannin tunkarar gasar Olympics da za ta fara yi a ranar Litinin.

Tawagar ta kunshi ‘yan wasa 20 daga cikinsu 12 suna taka-leda a gida da kuma takwas wadanda ke murza-leda a waje, karkashin jagorancin Samson Siasia.

Bayan tawagar ta yi wasanni a Korea, za ta koma Manchester domin yin atisaye daga nan kuma za ta nufi Amurka, sai kuma Brazil domin buga gasar Olympic a fagen kwallon kafa

Nigeria tana rukuni na biyu ne da ya kunshi Sweden da Colombia da kuma Japan.

Ga ‘yan wasa 20 da da suke tare da tawagar Nigera:

1. Emmanuel Daniel

2. Yusuf Mohammed

3. Emmanson Daniel

4. Sincere Seth

5. Ndifreke Effiong

6. Segun Oduduwa

7. Stanley Amuzie

8. Julius Emiloju

9. Erhun Obanor

10. Saturday Erimuya

11. Azubuike Okechukwu

12. Usman Mohammed

13. Stanley Dimgba

14. Sodiq Popoola

15. Saviour Godwin

16. Taiwo Awoniyi

17. Ubong Ekpai

18. Abdulrahman Taiwo

19. Nathan Oduwa

20. Tiongoli Tonbara