Rashford na daf da tsawaita zamansa a United

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dan wasan Manchester United, Marcus Rashford

Manchester United na daf da sanar da sake kulla yarjejeniyar ci gaba da buga mata wasanni da za ta yi da matashin dan kwallonta Marcus Rashford.

Sauran shekara daya ta rage tsohuwar kwantiragin da ya kulla ta kare da United, amma an warwareta za kuma su cimma wata sabuwa da zai dunga karbar fan dubu 20,000 a duk mako.

Kwallaye biyu ya ci wa United da fara buga mata tamaula a cikin watan Fabrairu a gasar Europa, inda ya ci FC Midtjyland da kuma wadda ya zura a gasar Premier kwanaki uku tsakanin

Haka kuma shi ne matashin dan wasa a tawagar Ingila da ya zura kwallo a raga, a kuma ranar Talata ne Ingila za ta fitar da sunayen ‘yan wasa 23 da za su wakilce ta a gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana.

Rashford din ya ci wa Manchester United kwallaye takwas a wasanni 18 tun daga lokacin da ya fara buga mata tamaula

Haka kuma United din tana tattaunawa da dan kwallon Kamaru, Borthwick-Jackson domin shi ma a tsawaita zamansa a Old Trafford.