Simeone zai auna makomarsa a Atletico

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kociyan Atletico Madrid, Diego Simeone

Kociyan Atletico Madrid, Diego Simeone ya ce zai auna makomarsa a kulob din, bayan da Real Madrid ta doke su a wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Asabar.

Madrid din ta ci Atletico 5-3 a bugun fenariti, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a karawar da suka yi a filin wasa na San Siro da ke Italiya.

Wannan shi ne karo na biyu da Real Madrid ta cinye Atletico Madrid a wasan karshe a gasar ta cin kofin zakarun Turai, inda aka ci Atletico 4-1 a shekarar 2014.

Simeone wanda ya fara horar da Atletico tun cikin shekarar 2011 ya ce rashin nasara a karawar karshe gazawa ce ga mai koyarwa.

Kociyan wanda ya jagoranci Atletico lashe kofin La Liga a shekarar 2014, an yi ta rade –radin cewar Chelsea na zawarcinsa, kafin daga baya ta nada Antonio Conte a matsayin wanda zai horar da ita a badi.

Bayan da Atletico ta kai was an karshe sau biyu a gasar zakarun Turai, Simeone ya jagoranci kulob din lashe Copa del Rey da Europa League da Uefa Super Cup da kuma Spanish Super Cup