Zika: Andy Murray zai nemi shawarar likitoci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Andy Murray bai yanke shawara kan halartar gasar Olympics a birnin Rio ba.

Fitaccen ɗan kwallon Tennis Andy Murray ya ce zai nemi shawarwarin likitoci a kan cutar Zika kafin ya tafi birnin Rio na ƙasar Brazil domin shiga gasar Olympics.

Ɗan wasan, mai shekara 29, ya ce zai ɗauki matakin ne saboda rahoton da masana kimiyya suka bayar cewa "bai kamata" a yi gasar ta Olympics da Paralympics ba saboda tsoron kamuwa da cutar.

Murray ya shaida wa BBC Radio 5 live cewa, "Zan yi magana da wasu likitoci a kan wannan batu domin na nemi shawararsu. Ina sa ran shiga gasar amma ban san haƙiƙanin abin da ke faruwa a Rio ba."

Ya ƙara da cewa: "Ina buƙatar samun ƙarin bayani kafin na yanke shawarar zuwa can."

Kwamitin da ke shirya gasar ta Olympic dai ya ce bai ga wani dalili da zai sa ya jinkirta gudanar da gasar ko ma ya soke ta a birnin na Rio ba, saboda tsoron kamuwa da ƙwayoyin cutar Zika, waɗanda ke sa ana haifar yara masu ɗan-kai.