Shari'ar Lionel Messi a kan haraji

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Ana tuhumar Messi da kin biyan haraji

A kasar Spaniya, a ranar Talata ne ake sa ran za a fara shari'a ga dan kwallon kafar Argentina, Lionel Messi, wanda har wa yau ke taka-leda a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, wanda ake tuhumarsa da kin biyan harajin da ya kai dala miliyon biyar.

Ana dai zargin Lionel Messi da hada baki da mahaifinsa wajen zille wa biyan harajin.

Mahukunta na zarginsu da boye dukiyarsu a Belize da kuma kasar Uruguay.

Ana dai sa ran za a kwashe kwana uku ana buga shari'ar.

Hukumar da ke tattara harajin Spaniya dai na bukatar a yi wa Lionel Messi da mahaifin nasa tara mai yawa, da kuma dauri.

Amma dan kwallon kafar da mahaifinsa sun musanta zargin da ake musu

Lionel Messi ya sha cewa shi ba wata harkar da ya sa a gaba dari bisa dari face kwallon kafa.

Kuma dukkan kudin da yake samu yana tsakaninsa ne da mahaifinsa, kuma da ya sanya hannu a kan kwangila gaba yake yi ba ya waiwaye.