Sturridge ya koma atisaye a tawagar Ingila

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan ya yi rauni ne a karawar da Sevilla ta doke Liverpool.

Daniel Sturridge ya koma yin atisaye a cikin tawagar kwallon kafa ta Ingila a ranar Litinin, domin tunkarar wasannin cin kofin nahiyar Turai.

Sturridge dan kwallon Liverpool bai buga wasan sada zumunta da Ingila ta ci Australia 2-1, sakamakon raunin da ya yi.

Dan wasan ya yi rauni ne a karawar da Sevilla ta doke Liverpool a wasan karshe a gasar Europa League.

Shi kuwa dan kwallon Southampton, Ryan Bertrand, bai yi atisaye da tawagar ba, sakamakon bugu wa da ya yi a kafarsa, amma likitoci sun duba lafiyarsa.

Sai dai kuma Gary Cahill ya murmure daga jinyar da ya yi, har ma ya yi atisaye da tawagar ta Ingila.

Tawagar ta Ingila za ta yi wasan sada zumunta da Portugal ranar Alhamis, daga nan ne za ta isa Faransa domin karawa da Rasha ranar 11 ga watan Yuni a gasar nahiyar Turai.