Super Eagles ta sauka a Luxembourg

Hakkin mallakar hoto the nff twitter
Image caption Nigeria na yin wasannin sada zumuntar ne da sabuwar rigar da za ta kaddamar.

Tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta isa Luxembourg a ranar Litinin, domin buga wasan sada zumunta da tawagar kasar a ranar Talata.

A ranar Juma’a tawagar ta Super Eagles ta doke ta Mali da ci daya mai ban haushi a wasan sada zumunta da suka kara a Faransa.

Rashin nasarar da Mali ta yi a hannun Super Eagles ita ce ta uku daga cikin wasanni 11 da ta fafata, duk da cewar ta samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a badi.

Nigeria na yin wasannin sada zumuntar ne da sabuwar rigar da za ta kaddamar wacce tawagar kasar za ta dinga yin amfani da ita a wasannin da za ta wakilce ta..

Tuni aka amince cewar tawagar matasa ‘yan kasa da shekara 23 ce za ta fara anfani da rigar a gasar wasannin Olympics da za a yi a Brazil a bana.