An fara yi wa Messi shari'a

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan shi ne lauya mai kare Messi

An fara sauraron shari'ar dan kwallon Barcelon Lionel Messi kan haraji a Sipaniya.

Ana tuhumar Messi da mahaifinsa Jorge, wanda ke kula masa da al'amuran kudinsa da zillewa biyan kasar Sipaniya harajin fiye da dala miliyan 4.5 tsakanin shekarun 2007 da 2009.

Hukumomi suna zarginsu da amfani da kasashen Belize da Uruguay inda ake zillewa biyan haraji domin boye kadarorinsu.

Hukumar karbar haraji ta Sipaniya na neman su biya tara mai dumbin yawa da kuma zama a gidan yari.

Amma dan kwallon kafar da mahaifinsa sun musanta zargin da ake musu.

Ana dai sa ran za a kwashe kwana uku ana buga shari'ar.

Lionel Messi ya sha cewa shi ba wata harkar da ya sa a gaba dari bisa dari face kwallon kafa.