Euro 2016: Rashford na cikin tawagar Ingila

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Rashford ya ci kwallo a wasan sada zumunta da Ingila ta doke Austarlia a ranar Juma'a.

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta saka sunan Marcus Rashford cikin ‘yan wasa 23 wadanda za su buga mata gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana.

Rashford dan kwallon Manchester United mai shekara 18, ya ci kwallo a wasan sada zumunta da Ingila ta doke Austarlia a ranar Juma’a.

A ranar Litinin Rashford ya tsawaita zamansa a United, inda zai ci gaba da murza-leda a Old Trafford har zuwa shekarar 2020.

Shi ma dan kwallon Liverpool, Daniel Stuuridge yana cikin tawagar, sai dai kuma Andros Townsend na Newcastle United da dan kwallon Leicester City, Danny Drink Water ba za su buga gasar bana ba.

Tawagar ta Ingila za ta buga wasan sada zamunta da Portugal a ranar Alhamis, domin shirin tunkarar gasar da Faransa za ta karbi bakunci.

Ingilar za ta fara karawa da Rasha a ranar 11 ga watan Yuni, sannan ta fafata da Wales ranar 16 ga watan, ta kuma yi wasan karshe na rukuni da Slovakia ranar 20 ga watan Yunin.

Ga jerin 'yan wasan:

Masu tsaron raga: Joe Hart (Manchester City), Fraser Forster (Southampton), Tom Heaton (Burnley).

Masu tsaron baya: Gary Cahill (Chelsea), Chris Smalling (Manchester United), John Stones (Everton), Kyle Walker (Tottenham Hotspur), Ryan Bertrand (Southampton), Danny Rose (Tottenham Hotspur), Nathaniel Clyne (Liverpool).

Masu was an tsakiya: Dele Alli (Tottenham Hotspur), Ross Barkley (Everton), Eric Dier (Tottenham Hotspur), Jordan Henderson (Liverpool), Adam Lallana (Liverpool), James Milner (Liverpool), Raheem Sterling (Manchester City), Jack Wilshere (Arsenal).

Masu cin kwallo: Wayne Rooney (Manchester United), Harry Kane (Tottenham Hotspur), Jamie Vardy (Leicester City), Daniel Sturridge (Liverpool), Marcus Rashford (Manchester United).