Ibrahimovic ba zai koma Malmo ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ibrahimovic ya ce zai fadi kungiyar da zai koma idan ya gaji da labaran da jaridu ke watsawa a kansa.

Zlatan Ibrahimovic ya ce ba zai koma kungiyar Malmo domin taka mata leda ba, amma zai iya buga gasar kasar Sweden.

Dan wasan, mai shekara 34 wanda Manchester United ke yin zawarci, kwantiraginsa ce ta kare da Paris St Germain a bana, ana kuma rade-radin zai iya komawa China da murza leda.

Ibrahimovic ya shaida wa ‘yan jarida cewa zai sanar da kungiyar da zai koma idan ya gaji da labaran rade-radin inda zai koma da buga wasanninsa.

Dan wasan ya fara buga kwallo a matsayin kwararren dan wasa a Malmo tsakanin shekarar 1996 zuwa 2004.

Daga nan ne kuma ya koma wasa a Ajax da Juventus da Inter Milan da Barcelona da kuma AC Milan, sannan ya je PSG a shekarar 2012.

Ibrahimovic yana cikin ‘yan wasa 23 da za su buga wa Sweeden gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Faransa a cikin wannan watan.