Lassana ba zai buga Euro 2016 ba

Hakkin mallakar hoto Getty

Lassana Diarra ba zai buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa gasar cin kofin nahiyar Turai ba, sakamakon jinya da yake yi.

Tuni kuma tawagar ta maye sunansa da na dan kwallon Manchester United, Morgan Schneiderlin.

Shi ma dan kwallon Real Madrid, Raphael Varane ba zai wakilci kasarsa a gasar da za ta karbi bakunci ba, sakamakon raunin da zai yi jinya tsahon makonni uku.

Faransar wadda Didier Deschamps ke horar wa ta maye gurbin Varane da dan kwallon Sevilla Adil Rami mai shekara 30.

Faransa wadda za ta yi bukin bude gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana ranar 10 ga watan Yuni, za kuma ta fafata da Romania a ranar.

Ga jerin ‘yan wasan kasar Faransa:

Masu tsaron raga: Hugo Lloris, Steve Mandanda, Benoit Costil.

Masu tsaron raga: Adil Rami, Laurent Koscielny, Eliaquim Mangala, Jeremy Mathieu, Patrice Evra, Bacary Sagna, Christophe Jallet, Lucas Digne.

Masu was an tsakiya: Paul Pogba, Blaise Matuidi, Morgan Schneiderlin, N'Golo Kante, Yohan Cabaye, Moussa Sissoko.

Masu cin kwallo: Antoine Griezmann, Dimitri Payet, Anthony Martial, Kingsley Coman, Olivier Giroud, Andre-Pierre Gignac.