Kuskure ne rashin zuwa da Drink Water Euro 2016 — Shearer

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shearer ya ce Roy Hodgson ya yi ganganci.

Tsohon dan kwallon Ingila, Alan Shearer, ya ce kociyan Ingila ya yi kuskure da ba zai je gasar nahiyar Turai da Danny Drink Water ba.

A ranar Talata ne mai horas da Ingila, Roy Hodgson ya sanar da sunayen ‘yan wasa 23 da za su wakilci kasar, kuma babu Danny Drink Water mai wasa a Leicester City a cikinsu.

Shearer ya ce kociyan ya yi ganganci da ya zabi ya tafi da Jack Wilshere da Jordan Henderson duk da basa kan ganiyarsu, maimakon ya dauki Drink Water.

Tawagar ta Ingila za ta buga wasan sada zamunta da Portugal a ranar Alhamis, domin shirin tunkarar gasar da Faransa za ta karbi bakunci a cikin watan nan.

Ingilar za ta fara karawa da Rasha a ranar 11 ga watan Yuni, sannan ta fafata da Wales ranar 16 ga watan, ta kuma yi wasan karshe na rukuni da Slovakia ranar 20 ga watan Yunin.