Dani Alves zai bar Barcelona

Dani Alves Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dani Alves ya shafe shekaru takwas a Barcelona

Barcelona ta sanar da cewar dan wasan kwallon kafar tawagar Brazil, Dani Alves, zai bar kungiyar.

Alves mai shekara 33, wanda ya koma Barcelona daga Sevilla a shekarar 2008, ya lashe kofunan zakarun Turai uku da na La Liga shida a kungiyar ta Spaniya.

Haka kuma ya dauki Copa del Rey sau hudu a Barcelona da kuma kofuna biyu da Barcelona ta ci a bana.

Alves wanda ya buga wa Brazil wasanni 89, yana da yarjejeniyar da ya kulla da Barcelona wanda za ta kare a Yunin 2007.

Daraktan Barcelona Fernandez ya sanar a shafin sada zumunta na Twitter kungiyar cewar dan kwallon ne da kansa ya nemi izinin zai gwada sa’a a wata kungiyar.

Ana sa ran Alves zai koma kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ke Italiya.