Kaka ba zai buga gasar Copa America ba

Image caption Amurka ce za ta karbi bakuncin gasar Copa America

Kaka ba zai buga wa Brazil gasar Copa America ba, sakamakon raunin da ya yi, za kuma a maye gurbinsa da Paulo Henrique Ganso.

Dan kwallon mai shekara 34, shi ne dan wasan Brazil na biyar da ba zai buga gasar ba, yayin da zai yi jinyar makonni uku.

Kaka tsohon dan kwallon AC Milan da Real Madrid, yana murza-leda ne a Orlando City mai buga gasar Amurka ta Major League.

Amurka ce za ta karbi bakuncin gasar Copa Amerika ta shekarar nan kuma ta 100 da fara ta, wadda za a bude a ranar Juma’a.

Brazil za ta fara wasa ne a ranar Asabar da Ecuador daga nan ta fafata da Haiti ranar 9 ga wata, sannan ta kece raini da Peru ranar 13 ga watan nan.