Fifa: Nigeria ta koma ta 12 a Afirka

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Duk shekara ne hukumar Fifa ke fitar da irin wannan mataki

Nigeria ta gusa sama zuwa mataki na 12 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka, sannan kuma ta 61 a duniya.

A jerin kasashen da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta fitar da suka fi iya murza leda a ranar Alhamis, ya nuna cewar har yanzu Super Eagles bata cikin goman farko a Afirka.

Nigeria wadda a watan Mayu ke matsayi na 67 a duniya ta samu gusawa sama ne bayan da ta ci Mali da Luxembourg a wasannin sada zumunta da suka yi.

Algeria ce ta ci gaba da zama a matsayinta na daya a Afirka, yayin da Argentina ke kan gaba a duniya wajen iya taka leda.

Kasashen da ke biye da Algeria a cikin goman farko da suka fi iya taka-leda a Afirka sun hada da Cote d’ivoire da Ghana da Senegal da Masar da Tunisia da tsibirin Cape Verde da Jamhuriyar Congo da Guinea da kuma Kamaru.