Man City ta dauki Gundogan

IIkay Gundogan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption IIkay Gundogan shi ne dan kwallon farko da Pep Guardiola ya saya

Manchester City, ta kulla yarjejeniya da IIkay Gundogan kan ya buga mata tamaula tsawon shekara hudu.

Gundogan zai koma City da murza-leda daga Borussia Dortmund, kuma shi ne dan wasa na farko da Pep Guardiola sabon kociyan kungiyar ya sayo.

Rahotanni na cewa City ta sayi dan wasan ne kusan kimanin fan miliyan 20.

Dan wasan tsakiyar na Jamus ya koma Dortmund ne daga Nuremberg a shekarar 2011.