Manyan jami'an Fifa sun 'bai wa kansu $80m'

Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto
Image caption Sepp Blatter da Valcke sun musanta zargin almundahana

Tsofaffin manyan jami'an hukumar kwallon kafa ta Fifa Sepp Blatter, Jerome Valcke da Markus Kattner sun yi wa kansu karin albashi da bai wa kawunansu kudaden lalita da su kai dala miliyan 80 a shekara biyar.

Fifa ta bayyana kwantiragin tsohon shugabanta Blatter, tsohon Skatare Valcke da tsohon Daraktan Kudi Kattner kwana guda bayan da 'yan sandan Switzerland suka kai samame ofishinta.

Lauyoyin hukumar sun ce akwai shaidun da ke nuna cewa mutane ukun sun yi yunkurin "azurta kawunansu" tsakanin shekarar 2011 da 2015.

An kwace takardu da wasu bayanai na kwamfiyuta a lokacin sumamen na ranar Alhamis, wadanda ke da alaka da Blatter da Valcke.

An dakatar da Blatter da Valcke daga harkokin wasanni na tsawon shekara shida da 12 bayan da aka same da laifin almundahana da kudaden Fifa.

Dukka mutanen biyu sun musanta aikata ba daidai ba.