Di Matteo ya zama sabon kocin Aston Villa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Di Matteo ya maye gurbin Remi Garde.

Aston Villa ta nada tsohon kociyan Chelsea, Roberto di Matteo, a matsayin wanda zai horar da ita tamaula.

Di Matteo ya maye gurbin Remi Garde, wanda aka sallama, bayan da kungiyar ta fadi daga gasar Premier da aka yi ta bana.

Di Matteo, wanda ya lashe kofin zakarun Turai a Chelsea a shekarar 2012, ya zabi Steve Clarke ya taimaka masa gudanar da aikin.

Rabonda Di Matteo mai shekara 52, tsohon kociyan West Brom da Schalke ya horar da kungiya tun cikin shekarar bara.

Aston Villa ce ta yi ta karshe ta ashirin a gasar Premier bana da aka kammala.