Carneiro ta ki sasantawa da Chelsea

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jose Mourinho shi ne zai jagoranci Manchester United a wasannin badi

Tsohuwar likitan Chelsea, Eva Carneiro ta ki karbar tayin kudi fam miliyan 1.2 da kungiyar ta yi mata tayin za ta biya ta.

Hakan na kunshe ne a cikin wasu takardun kama aiki da ta mikawa kotun sauraren karar ma'aikata.

Caeneiro na tuhumar tsohuwar kungiyarta da shirya makarkashiyar da aka sallameta daga aiki.

Haka kuma tana son a saurari karar da ta kai Jose Mourinho tana zarginsa da cin zarafi da nuna banbanci.

Lawyan Carneiro ya ce Mourinho zai gurfana a gaban kuliya domin amsa tambayoyi tsawon wuni guda.

Ana sa ran za a saurari karar daga tsakanin kwanaki bakwai zuwa 10 a wata kotun saurarar karar ma'aikata da take Croydon.

Chelsea da Mourinho sun yi tayin bai wa Carneiro kudi fam miliyan 1.2, domin kawo karshen diyyar da take nema.