Man City za ta kara da Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Guardiola ne ya maye gurbin Pellegrini a Manchester City

Sabon kocin Manchester City, Pep Guardiola zai jagoranci kungiyar karawa da Bayern Munich a wasan sada zumunta.

Guardiola tsohon wanda ya horar da Bayern Munich zai yi wasansa na farko a City ne ranar 20 ga watan Yuli.

A karshen kakar bana ne Guardiola, wanda ya dauki kofuna uku na Bundesliga da guda biyu na Kalubalen Jamus a Munich, ya maye gurbin Manuel Pellegrini.

Karawar da za a yi a Allianz Arena ita ce ta farko da Carlo Ancelotti wanda ya maye Pep Guardiola zai ja ragamar Munich.

Kwanaki biyar tsakani City za ta yi gumurzu da Manchester United a Beijing.