Ronaldo ya fi bayar da kwallaye a ci a raga

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Real Madrid ce ta lashe kofin zakarun Turai na bana kuma na 11 jumulla

Cristiano Ronaldo ne ya zama wanda yafi bayar da kwallaye aka ci a raga a bana a Real Madrid.

Ronaldo ya bayar da kwallaye 10 ga abokan wasansa da suka ci a raga a gasar La Liga, ya kuma taimaka aka ci uku a gasar zakarun Turai.

Karim Benzema da Gareth Bale ne suka fi amfana da kwallayen da Ronaldo ya ba su suka ci a raga, kowannensu ya ci uku-uku.

Ronaldo dan kwallon kafar tawagar Portugal, ya ci kwallaye 51 daga wasanni 50 da ya buga a bana.

Bayan Ronado, Gareth Bale ne na biyu a matsayin wanda ya taimaka aka ci kwallaye a Madrid, ya bayar da 11.

James Rodriquez da Isco sun bayar da kwallaye goma-goma da aka ci a raga a kakar bana da aka kammala.