Everton ta dauki koci Koeman

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Shekara biyu Koeman ya yi yana horar da Southampton

Everton ta amince da kulla yarjejeniyar daukar kociyan Southampton, Ronald Koeman domin ya zama sabon kociyanta.

Everton za ta biya Koeman wanda ya jagoranci Southampton shekara biyu kudi kusan fam miliyan biyar.

Kafin a kammala gasar wasannin bana Everton ta kori kociyanta Roberto Martinez daga aiki.

Matsayi na 11 Everton ta kare a kan teburi a bana, bayan da Martinez ya yi alkawarin kai kungiyar gasar cin kofin zakarun Turai, a lokacin da aka bashi aikin.

Southampton kuwa mataki na shida ta yi a gasar Premier da aka kammala karkashin Koeman, za kuma ta buga gasar zakarun Turai ta Europa.