Vardy ya maida hankali kan gasar Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ingila za ta fara karawa da Rasha a ranar Asabar a gasar cin kofin nahiyar Turai

Wakilan Jamie Vardy, sun sanarwa da Arsenal cewa dan wasan na son ya maida hankalinsa a gasar cin kofin nahiyar Turai.

Arsenal din na son daukar dan kwallon Leicester City, ana kuma cewa ta yi shirin biyansa albashin fan 120,000 a duk mako.

Leicester City wadda ta lashe kofin Premier bana, ta yi wa Vardy kari a kan tayin da Arsenal ta yi domin kar ya bar kungiyar.

Tun a ranar Litinin Arsenal ta yi dakon dan wasan ya amince da cewar zai murza-leda a Emirates, kan yarjejeniyar fan miliyan 20.

Yanzu haka dan kwallon yana tare da tawagar Ingila a Faransa, domin tunkarar wasannin gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana.

Tuni kuma kociyan Ingila, Roy Hodgson ya ce ba zai amince da 'yan wasa su dinga maganar kungiyoyinsu ba, domin zai iya raba kan 'yan wasa.