An bukaci a tuhumi Neymar a gaban kotu

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Tuni aka fara sauraren karar da ake zargin Messi da kaucewa biyan haraji a Spaniya

Masu shigar da kara a Spaniya sun yi kira da a gurfanar da Neymar a gaban kotu kan zargin zamba.

Masu shigar da karar daga manyan kotunan aikata laifuffuka na Spaniyar sun zargi Neymar da mahaifinsa da boye hakikanin yawan miliyoyin kudin da aka saye shi daga Santos zuwa Barcelona.

A hirar da aka yi da Neymar ya karyata aikata ba daidai ba.

An fara yi wa Messi shari'a

Barcelona ta ce ta sayi Neymar a shekarar 2013 kan kudi Yuro miliyan 57, daga cikin kudaden Neymar da mahaifinsa mai kula da harkokin wasanninsa suka karbi Yuro miliyan 40, aka bai wa Santos Yuro miliyan 17.

Masu shigar da karar sun ce kudin ya kusan kai Yuro miliyan 83, kuma Barcelona ce ta boye wani sashi na yarjejeniyar.

Sai dai kuma Barcelona ta karyata yin rufa-rufa kan cinikin dan kwallon tawagar Brazil din.