Wikki za ta kara da El-Kanemi ranar Laraba

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Za a buga wasannin mako na 21 a gasar ta Firimiyar Nigeria ranar Laraba

Ranar Laraba ne za a ci gaba da wasannin mako na 21 a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria.

Daga cikin wasanni takwas din da za a fafata a ranar, Wikki Tourist za ta karbi bakuncin El-Kanemi Warriors a Bauchi.

Kano Pillars kuwa za ta ziyarci Enugu ne domin karawa da Rangers, da fafatawa tsakanin Warri Wolves da Heartland.

Ita kuwa Akwa United za ta karbi bakuncin Sunshine Stars ne, yayin da Lobi Stars da Shooting Stars za su kece raini a Makurdi.

Sai a ranar Alhamis ne za a yi gumurzu tsakanin Enyimba da Rivers United a Aba.

Ga jerin wasannin da za a buga:
  • MFM FC da Nasarawa FC
  • Lobi Stars da Shooting Stars FC
  • Akwa United da Sunshine Stars FC
  • Abia Warriors da Ikorodu United FC
  • Warri Wolves da Heartland FC
  • Rangers da Kano Pillars
  • Niger Tornadoes da Plateau United FC
Ranar Alhamis:
  • Enyimba da Rivers United