Tah ya maye gurbin Rudiger a tawagar Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Lahadi Jamus za ta fara wasan farko da Ukraine

Tawagar kwallon kafa ta Jamus, ta gayyaci Jonathan Tah, domin ya maye gurbin Antonio Rudiger wanda ya ji rauni a wajen atisaye.

Rudiger ya ji rauni ne a ranar Talata lokacin da tawagar Jamus ke yin atisayen tunkarar wasannin gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana a Faransa.

Tah mai shekara 20, ya yi Jamus wasan farko kuma tilo da ya buga a wasan sada zumunta da Ingila a cikin watan Maris.

'Yan kwallon da za su tsare wa Jamus baya daga tsakiyar fili a gasar ta Faransa sun hada da Jerome Boateng da Mats Hummels da kuma Shkodran Mustafi.

Jamus za ta fara karawa da Ukraine a gasar cin kofin nahiyar Turai a ranar Lahadi.