Man United ta dauko Eric Bailly

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bailly shi ne dan wasa na farko da Mourinho ya saya a United

Manchester United ta kulla yarjejeniyar daukar Eric Bailly, domin ya taka mata- leda idan ya samu takardun izinin zama a Turai.

Eric dan kasar Ivory Coast, zai je Old Tarfford ne kan kudi fam miliyan 30 a kwantiragin shekara hudu.

Bailly dan kwallon Villareal ya yi wasanni 40 a gasar Laliga, guda biyar din farko ya yi su ne a Espanyol.

Dan wasan ya koma taka-leda a Villareal kan kudi fam miliyan hudu da dari hudu a watan Janairun 2015.

Erik ya buga wa Ivory Coast dukkan wasannin da ta lashe na kofin nahiyar Afirka a shekarar 2015 wanda aka yi a Equatorial Guinea.