Ronaldo ya fi 'yan wasa samun kudin shiga

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ronaldo yana cikin tawagar kwallon kafa ta Portugal a gasar cin kofin nahiyar Turai

Cristiano Ronaldo ne dan kwallon da ya fi samun kudin shiga a fagen wasanni a duniya, in ji mujallar Forbes.

Mujallar ta ce Ronaldo ya samu fam miliyan 60 da dubu dari shida a bara, daga albashin da ya karba da ladan wasa da kuma tallace-tallace.

Sama da shekara 10 da rabi Floyd Mayweather da Tiger Wood ne suke yin kaka-gida a matsayi na daya a jerin wadanda suka fi samun kudin shiga a fagen wasanni a duniya.

Ronaldo ya samu damar dare wa mataki na daya ne, sakamakon ritaya da Mayweather, zakaren damben boksin da rashin buga wasan kwallon golf da Wood ke yi sakamakon rauni akai-akai.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi, shi ne na biyu a jerin wadanda suka fi samun kudin shiga a duniya a bangaren wasanni.

Messi dan kwallon Argentina, ya karbi zunzurutun kudi a bara da suka kai fam miliyan 56 da dubu dari daya.

Ga jerin 'yan wasa 10 da suka fi arziki a duniya:
  1. Cristiano Ronaldo - Kwallon kafa ($88m/£60.6m)
  2. Lionel Messi - Kwallon kafa ($81.4m/£56.1m)
  3. LeBron James - Kwallon raga ($77.2m/£53.2m)
  4. Roger Federer - Kwallon tennis ($67.8m/£46.7m)
  5. Kevin Durant - Kwallon raga (£56.2m/£38.7m)
  6. Novak Djokovic - Kwallon tennis ($55.8m/£38.46m)
  7. Cam Newton - Kwallon zari ruga ta Amurka ($53.1m/£36.6m)
  8. Phil Mickelson - Kwallon golf ($52.9m/£36.46m)
  9. Jordan Spieth - Kwallon golf ($52.8m/£36.39m)
  10. Kobe Bryant - Kwallon kwando ($50m/£34.46m).