'Tawagar Wales ba ta dan wasa daya ba ce'

Hakkin mallakar hoto huw evans picture agency
Image caption Bale ya lashe kofin zakarun Turai na bana a Real Madrid

Gareth Bale ya karyata batun da ake cewar tawagar kwallon kafa ta Wales ta dan wasa daya ce.

Wales tana daga cikin kasashen da za su fafata a gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Faransa a bana.

Kuma Wales din za ta fara wasanta na farko a gasar da Slovakia a ranar Asabar.

Ana ta cewa Bale shi ne kashin bayan tawagar ta Wales, bayan da ya ci kwallaye shida daga cikin 11 da kasar ta ci a wasannin shiga gasar.

Bale dan kwallon Real Madrid ya ce kan tawagar a hade yake kamar 'yan uwa, kuma a fagen tamaula suna mayar da hankalinsu kan lashe wasa.

Wannan ne karon farko da tawagar Wales za ta buga babbar gasa, bayan gasar cin kofin duniya da ta halarta a shekarar 1958.