Carrick ya sabunta zamansa a Old Trafford

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Carrick ya koma United a shekarar 2006 daga Tottenham

Michael Carrick ya cimma yarjejeniyar ci gaba da buga tamaula a Manchester United tsawon shekara daya.

Carrick mai shekara 34, ya koma United a cikin watan Yunin shekarar 2006 daga Tottenham.

Dan wasan ya buga wa Manchester United wasanni 42 a kakar wasannin da aka kammala, amma kuma bai ci kwallo ko daya ba.

Carrick ya ce ya yi murna da zai ci gaba da buga wa United wasanni, a karkashin Jose Mourinho.

Daga karshe ya kuma gode wa magoya bayan United da suke mara masa baya kan yadda yake murza-leda.