Fletcher da Wes Brown za su bar Sunderland

Wes Brown Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wes Brown ya shafe shekaru biyar a Sunderland

Steven Fletcher da Wes Brown na daga cikin 'yan wasa hudu da kulob din Sunderland ya sallama.

Ragowar mutane biyun sun hada da dan wasan gaba Danny Graham da kuma mai tsaron gida Steve Harper.

Fletcher, mai shekaru 29, dan kasar Scotland, wanda ya je kungiyar daga Wolves kan kudi fan miliyan 12 a shekara ta 2012, ya kare kakar bana ne a matsayin aro a kulob din Marseille.

Shi ma Graham, mai shekaru 30, yana aro ne a kungiyar Blackburn Rovers.

Shi kuwa tsohon dan wasan Man United Brown, mai shekaru 36, ya shafe shekaru biyar a Sunderland, yayin da Harper, mai shekaru 41, ya bar kungiyar bayan watanni 12.

Fletcher ya zura kwallaye 23 a wasanni 108 a Sunderland, kuma a baya ya taka leda a Burnley da Hibernian.

Da kyar Sunderland ta sha a kakar wasannin da ta kare.