De Gea ya musanta shirya fatin karuwai

David de Gea Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption De Gea na cikin masu tsaron gidan da suka fi kwarewa a duniya

Mai tsaron gidan Spaniya David de Gea ya musanta zargin cewa ya shirya wani fati na karuwai, inda aka tilastawa wata mata yin lalata ba a san ranta ba.

Dan wasan na Manchester United ya shaida wa manema labarai cewa "wannan zunzurutun karya ce.

Zargin ya bayyana ne a wasu takardun kotu a wata shari'a da ake yi wa wani babban mai watsa hotunan batsa.

Wata jarida ce a kasar ta Spaniya ta samu takardun kotun.

Wani mai bayar da shaida ya ce mutumin ya tilastawa matar da kuma wata yarinya saduwa da wasu 'yan wasan tawar Spaniya 'yan kasa da shekaru 21 a shekarar 2012.

Dan wasan na cikin tawagar Spaniya da yanzu haka ke kasar Faransa domin shirin kare kanbunsu a gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2016.