Euro 2016: An kama wani mai goyon bayan Ingila

Euro 2016 Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An tsaurara matakan tsaro a filayen kasar baki daya

'Yan sanda a Faransa sun kama wani mai goyon bayan Ingila sakamakon wani hargitsi da ya barke a birnin Marseille.

An kuma kama wani mazaunin birnin - sai da 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye.

Wani jami'in dan sanda na Birtaniya a garin, ya ce hatsaniyar ta barke ne tsakanin mazauna birnin da kuma magoya bayan Ingila.

'Yan sanda sun ce an shawo kan lamarin na ranar Alhamis cikin sauri.

Hargitsin ya faru ne a wajen wata mashaya a yankin Old Port na birnin da misalin karfe 12 na dare.