Za a fara gasar cin kofin Euro 2016

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fiye jami'an tsaro 90,000 ne za su yi aiki domin kare 'yan kallo

A ranar Juma'a ne za a fara gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai ta Euro 2016, inda mai masaukin baki Faransa, za ta kara da Romania a birnin Paris.

An tsaurara matakan tsaro yayin da kasar ke cikin dokar ta baci tun bayan harin da kungiyar IS ta kai a watan Nuwamban bara, wanda ya kashe mutane 130.

Fiye da 'yan sanda 90,000 da sojoji da jami'an tsaro masu zaman kansu ne za su yi aiki domin kare 'yan kallo miliyan bakwai da ake sa ran za su halarci gasar.

Gwamnatocin Amurka da na Birtaniya duka sun gargadi magoya baya cewa za su iya kasancewa cikin hadari.

Sai dai Hukumar Kwallon Kafa ta Turai UEFA da gwamnatin Faransa sun ce sun shirya tsaf domin kare 'yan kallon da za su halarci wasanni 51 da za a fafata.Euro 2016