Tarihi da nasarorin Amodu Shu'aibu

Amodu Shu'aibu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amodu Shu'aibu ya rasu yana da shekaru 58

An haifi marigayi Amodu Shu'aibu a ranar 18 ga watan Afrilu na shekarar 1958 a garin Okpella na jihar Edo a Kudancin Najeria.

Tauraruwarsa ta fara haskawa a fagen kwalon kafa a lokacin da ya jagoranci kulob din BCC Lions na garin Gboko in da suka lashe kofin kulob-kulob na Afrika a 1990.

Kulob din ya sake kaiwa matakin karshe a gasar, sai dai kuma kulob din Dynamos na Zambia ya samu nasara akansu da ci 5-4 a shekarar 1991.

Bayan shekaru uku, Amodu ya maye gurbin kocin Najeriya Clemens Westerhof a shekarar 1994, inda ya jagoranci zakarun Afrikar zuwa gasar cin kofin nahoyoyi a kasar Saudiyya. Daga nan kuma sai ya bar tawagar.

Ya sake dawowa domin jan ragamar kungiyar ta Najeriya daga shekarar 1998 zuwa 1999, 2001-2002 da kuma 2008-2010.

Ya taimaka wajen ganin 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya sun samu nasarar zuwa gasar cin kofin duniya a shekarar 2002 wanda aka yi a Japan da Koriya ta Kudu, sannan ya jagorance su sun kai mataki na uku a gasar cin kofin kasashen Afrika a Mali a 2002.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau hudu Shu'aibu na jagorantar Super Eagles

A karkashin jagorancinsa, Najeriya ta samu ikon zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 2010, wanda aka yi a Afrika ta Kudu, sai dai kuma an kore shi duk da cewa kasar ta kare a mataki na uku a gasar cin kofin kasashen Afrika da aka yi a Angola.

Wannan shi ne karo na biyu da aka cire shi daga mukaminsa gabanin buga wasan cin kofin kwallon kafa na duniya.

Duk da irin nasarorin da ya samu a Super Eagles, Amodu ya fuskanci rashin jituwa da magoya bayan kungiyar da kuma wadanda suka dauke shi aiki, inda masu sharhi ke kushe tsarin taka ledarsa.

Ya lashe kofuna da dama

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta nada shi a matsayin daraktan a shekarar 2013, amma kuma ba a tabbatar da shi ba sai a 2014.

Amodu yakasance wanda abokan aiki ke girmama wa, mutum ne d ya san ya kamata wanda kuma ya ke da kwarewa a kan wasanni, kuma a koda yaushe ba ya shiru a kan abin da ya ga ya dace ya yi magana.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amodu ya lashe kofuna da dama a gasar cikin gida ta Najeria

A hirar sa ta karshe da sashen wasanni na BBC a watan Maris, Amodu ya bayyana irin matsalolin da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ke fuskanta, inda ya ce zai zauna da masu ruwa da tsaki wajen lalubo hanyoyin magance su.

"Daga cikin matsalolin akwai rashin kyakkyawan tsarin gudanar da kwallan kafar da kuma daukar nauyinta," a cewarsa.

Amodu ya fara harkar koci ne a kulob din BBC Lions, sannan ya koma El-Kanemi Warriors, kuma ya fi kowa lashe kofina a gasar cikin kofin FA na Najeria, inda ya samu nasara a 1989, 1992, 1993 and 1994.

Ya samu nasarar daukar gasar League da kofin kalubale har sau biyu da Super Cup sau uku a shekarun 1989, 1993 and 1994.

Ya kuma horas da kulob din Orlando Pirates na kasar Afrika ta kudu tsakanin shekarar 1996 da 1997.