Murray zai kara da Mahut a gasar Aegon

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Murray dan wasan kwallon tennis din Birtaniya

Andy Murray zai fafata da Nicolas Mahut a gasar kwallon tennis ta Aegon da za su yi gumurzu ranar Litinin a Queen's Club.

Idan har Murray ya samu nasara a wasan, zai fuskanci Aljaz Bedene ne a wasan zagayen gaba a gasar.

Shi kansa Bedene din sai ya doke Benoit Paire, wanda ya maye gurbin Jo-Wilfried Tsonga kafin ya yi gumurzu da Murray.

A kuma ranar Litinin din ne Stan Wawrinka zai fafata da Fernando Verdasco.