Nasarawa ta doke IfeanyiUbah da ci 4-2

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sakamakon wasannin mako na 22 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Nasarawa United ta hada maki uku a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da ta doke IfeanyiUbah da ci 4-2 a wasan mako na 22 da suka yi a ranar Lahadi.

Minti 17 da fara wasa Esosa Igbinoba ya ci wa Nasarawa United kwallo, sannan ya kara ta biyu a bugun fenariti, a kuma minti na 30 ne Nasarawa ta ci gida ta hannun Samson Gbadebo,

Bayan da aka dawo daga hutu Nasarawa ta ci ta uku ta hannun Abdulrahman Bashir da kuma ta hudu ta hannun Tayo Fabiyi.

IfeanyiUbah ta kare zare kwallo daya ta hannun Okereke Maduabuchi saura minti 11 a tashi daga fafatawar.

Ga sakamakon wasu wasannin da aka buga:
  • Kano Pillars 2-2 Warri Wolves
  • Ikorodu Utd 1-1 Akwa Utd
  • Heartland 0-0 Wikki
  • Shooting Stars 1-0 Enyimba
  • Rivers United 4-1 MFM