U-20: Nigeria za ta fafata da Sudan

Hakkin mallakar hoto The NFF
Image caption Nigeria ce za ta fara ziyartar Sudan a wasan farko

Tawagar kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekara 20 ta Nigeria za ta fafata da Sudan a zagayen kashe na wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Nigeria ta samu wannan matsayin ne bayan da ta doke tawagar Burundi da ci 2-1 a fafatawar da suka yi a Calabar ranar Asabar.

Nigeria ta ci kwallayenta ne ta hannun Victor Osimhen da kuma kyaftin din tawagar Kelechi Nwakali, yayin da Burundi ta ci na ta kwallon ta hannun Magloire Ndikumana.

A karawar farko da tawagogin biyu suka yi makonni uku da suka wuce a Bujumbura, Nigeria ce ta samu nasara da ci daya mai ban haushi.

Zambia ce dai za ta karbi bakuncin gasar wadda za a yi a shekarar 2017.