Riise ya yi ritaya daga buga tamaula

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon dan wasan tawagar Norway da Liverpool mai tsaron baya

Tsohon dan wasan tawagar Norway da kungiyar Liverpool, Arne Riise ya yi ritaya daga buga tamaula yana da shekara 35 da haihuwa.

Dan wasan wanda ke kan gaba wajen yawan buga wa tawagar Norway wasanni ya soke yarjejeniyar da ya kulla da kungiyar Aalesund ta Norway nan take.

Bayan da Riise ya zama kwararen dan kwallon kafa a Aalesund a shekarar 1996, daga nan ne ya yi wa Monaco wasanni shekara uku, sannan ya koma Liverpool a shekarar 2001.

Dan kwallon ya buga wa Liverpool wasanni 339 ciki har da wanda suka ci AC Milan a Santanbul a gasar cin kofin zakarun Turai a 2005, da kofin kalubalen Ingila da suka ci West Ham, daga nan ne ya koma Roma a shekarar 2008.

Kuma a shekarar 2011 ya koma Fulham da murza-leda, sannan a shekarar 2014 ya dan yi wasanni a Apoel Nicosia da kuma Delhi Dynamos.

A cikin watan Maris ne Riise ya koma wasa a kungiyar da ya fara murza-leda tun yana dan karaminsa.