An fitar da Brazil daga Copa America

Brazil da Peru Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ba karamin koma baya ba ne ga Brazil

An fitar da Brazil daga gasar cin kofin Copa America bayan da Peru da doke ta da ci daya mai ban haushi.

Wannan ne karo na farko da aka cire kasar a rukunin farko na gasar cikin shekaru kusan 30.

Brazil, wacce ta lashe kofun duniya sau biyar, ta shafe wasa 16 ba tare da ta yi nasara a kan Peru ba.

Raul Ruidiaz ne ya zura kwallon a minti na 75, inda 'yan Brazil suka yi korafin cewa kwallon ta taba hannun sa kafin ya ci.

Ecuador ta lallasa Haiti da ci 4-0 abin da ya ba ta damar zuwa zagayen dab da na kusa da na karshe a karon farko tun shekarar 1997.

Wannan rashin nasara ta sa an fara rade-rade kan makomar kocin Brazil Dunga.

Sai dai tsohon kyaftin din kasar ya ce: "Mutuwa kawai na ke tsoro, amma ba na tsoron makoma ta".