An daure magoya bayan Ingila biyar a Faransa

Image caption An gargadi Rasha da Ingila kan za a korarsu daga gasar nahiyar Turai idan suka kara tada yamutsi

Kimanin magoya bayan tawagar Ingila biyar ne aka daure a gidan yarin Faransa, saboda samunsu da laifin jifan 'yan sanda da kwalabai.

Haka kuma za a gurfanar da wani magoyin baya daya, domin a yanke masa hukuncin da ya kamace shi.

Masu shigar da kara a Faransa sun ce ana tsare da magoya bayan tawagar Rasha, wadanda suka yi shiri na musamman kan hatsaniyar da ta barke tun kafin karawa da Ingila da wadda aka yi bayan wasan.

An kama magoya bayan Rasha da dama wadanda suka shiga cikin filin wasa da kuma wadanda aka tsare a wajen filin.

Sama da 'yan kallo 35 suka samu munanan raunuka, kuma da dama daga cikin magoya bayan Ingila ne.

Haka kuma an kama mutane 20 'yan Ingila da ake tuhuma da tada yamustin kwanaki ukun da aka yi ana yi a biranen Farnasa.