An tabbatar da korar Giwa FC a gasar Nigeria

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Saura kungiyoyi 19 ne suke buga gasar Firimiya ta bana

Kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafa ta Nigeria ya amince da hukuncin da aka kori kungiyar Giwa FC daga buga gasar Firimiyar kasar.

Hukumar gudanar da gasar kasar ce ta sallami kungiyar Giwa FC daga buga wasannin Firimiya a cikin watan Mayu, bayan da ta karya dokar kin halartar wasanni uku na gasar.

Kungiyar ta Giwa ba ta je karawa da Wikki Tourist ba da fafatawa da Akwa United da kuma wasa da Enyimba.

An hukunta Giwa FC da komawa buga wasanni uku Ilorin bayan da aka samu hatsaniya a karawar da ta karbi bakuncin Enugu Rangers a Jos.

Kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafar ya amince da Giwa FC ta biya Naira miliyan 10, da kuma biyan dubu 650 kudaden ladan alkalan wasan da kungiyar ba ta je wasannin ba.

Haka kuma Giwa FC za ta biya Naira miliyan daya ga Enyimba, kudin jigilar da kungiyar ta yi ta shirin karawa a wasan.

Kwamitin ya kuma ce kungiyar ta Giwa ba ta je gabansa domin kare kanta ba.