An ci kwallaye 431 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto npfl Twitter
Image caption An buga wasannin mako na 22 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Kwallaye 431 aka ci a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka yi wasanni 197.

A karshen mako ne aka buga wasannin sati na 22 a gasar, inda aka ci kwallaye 23, guda shida daga ciki kungiyoyin da suka buga wasa a waje ne suka ci.

Kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist ta garin Bauchi ce wadda tafi cin kwallaye a gasar, inda ta ci 30, kuma ita ce wadda ke da karancinsu a raga, inda aka ci ta 12.

Ana buga gasar bana ne da kungiyoyi 19, bayan da aka kori Giwa FC daga wasannin, saboda karya dokar kin buga wasanni uku a gasar ta Firimiya.